BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na tara
Ko ya halasta na ba yaro nono alhalin ina cikin janaba?
TAMBAYA: Akramakallah. Ko Sista za ta iya bude gidan sayar da abinci, kuma ya zama ita za ta sayar da kanta?
Daga Nura Yahya Mai wada Shuwaki jihar Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To, akwai ka'idodi dai na hulda da mutane, tsakanin maza da mata ne, ko mata ya su-ya-su, ko maza ya-su-ya-su. Saboda haka abin da za mu ce kawai shi ne wadannan ka'idodin ya kamata ta san su, ya zama su ta kiyaye. Kamar yadda ya zo cewa; kada dayanku ya aikata aiki sai ya san hukuncin Allah a cikinsa. Saboda haka sai ta san menene haram da halas a sana'ar sayar da abincin. Amma dai in dai ta yi abinci ne ta sayar, ya halatta. Sai dai dole ta bi ka'idodi. Sai ta nemi sanin menene ka'ida wanda ya shafi wannan aiki khasatan ?
TAMBAYA: Idan an sami irin mummunan hatsarin motan nan, sai ya zamana an kasa tantancewa tsakanin musulmi da kafiri. Ko yaya za a yi?
Daga Nura Yahya Mai wada Shuwaki jihar Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To ai wannan ya sha ma faruwa, kuma irin shi akan yi masu salla ne a bizne su kuma a makabartar musulmi, ko da za a yi masu rami gaba daya ne. In dai da musulmi a cikinsu, sai ya zama su wadanda suke ba musulmin ba sun raka musulmi din. Wala'alla yana nufin siffarsu ta caccanza har ba za a iya binne jikin wani ba tare da wani ba. Ko kuma kuna ko abin da ya yi kama da haka nan. Ala ayyi halin, in dai akwai 'ishtibahi' tsakanin musulmi da kafirai, to dole kawai a yi masu daukar su musulmi ne. Har da kafiran. Saboda haka sai ya zama za a yi masu wanka da likkafani da salla, kuma a bizne su a makabartar musulmi. Amma wajen sigar salla, sai a yi da nufin musulmin cikinsu ake nufi. Ka ga su wadannan sun zama tamkar wadansu tarkace da suka raka musulmi kabari din.
TAMBAYA: Mutum ne ya wakilta wani a kan zai sayar masa da babur misali, sai shi wanda aka wakilta din ya samo wanda zai saya, amma ya kara wani abu a kan kudin da shi mai babur din ya ba da sallamin mashin din. To ko shi ya halasta ya ci wannan abin da ya kara din, duk da cewa kuma mai mashin din zai ba shi wani abu a cikin kudin da ya yi masa sallamin mashin din.
Daga Musa Alhasan, Unguwar Mu'azu, Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: To ya danganta da yadda suka yi sigar cinikin ne. In ya ce masa ga babur dina ka sayar ne, to duk yadda ya sayar kudin mai babur ne. In kuwa tun farko ya ce masa ka sayar kaza, duk abin da ya hau naka ne, sun yi dama dawajewa a haka nan, to wannan kuwa. Amma in dai ya ce masa ya sayar masa ne kawai, to lalle duk yadda ya sayar, duk kudin na mai babur ne. Shi kuma alabasshi a ba shi lada. Amma bai halatta gare shi ya karbi wani kudi na daban ya boye wa mai kaya ba, saboda hakkin mai kayan ne.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ya nemi auren wata, har ya dauki hotunansa ya ba ta, ita ma ta ba shi nata, sai aka kada shi. Shin ya halatta ya ci gaba da rike hotunan nan nata, ita ma ta rike nasa?
Daga Garba Ibrahim Kafinta Misau jihar Bauci
SHAIKH ZAKZAKY: To, da ma dai dole ne ya zama akwai hijabi. Idan hotuna ne wadanda suke akwai hijabobi, wato abin da ya bayyana kawai shi ne wanda ya halatta a gani, to zai zama babu laifi da shi. Amma idan hotunan ba hijabi, to tun farko da ma bai halatta gare shi ya mallaki hoton ba. Saboda haka wannan dole ya mayar mata da kayanta, ba zai halatta gare shi ya rike hotuna din ba. In ba ta hijabi din nan, da ma tun asali ka ga an yi laifi kenan. Amma in tana da hijabi shi kenan ba wani laifi. Sai dai abin da ya fi dai tunda ba shi da wata bukata dangane da al'amarinta ka ga sai ya sallama mata kayanta. Shi ma shi ya fi, ko da tana da hijabin.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne aka daura masa aure, sai ya mutu tun kafin a kai amarya. Shin matar za ta yi takaba kuma za ta ci gadonsa?
Daga Babangida Abubakar Mai shidda kasuwar Misau jihar Bauci
SHAIKH ZAKZAKY: Sai mu ce masa eh! Haka din ne. Abin da ake nufi da takaba shi ne ta zauna cikin reshin ado da kamanninta mai bakin ciki har wannan adadin. Sannan kuma tana da gadonsa.
TAMBAYA: Me mutum zai yi lokacin da ya kama matarsa da kwarto?
Daga Mustafa Ahmad Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: To tunda shi kadai ne sai dai li'ani. Abin da zai iya yi kawai a shari'a shi ne li'ani, tunda shi ya gani ba kuma zai iya kawo shaidu uku tare da shi ba. Sai dai ya yi li'ani. Sai ya je ya kai ta kara ya ce ta yi zina tunda shi mijinta ne, in ta yarda ta yi zina sai a yi mata hukunci. In ta ce ba ta yi ba sai su yi li'ani. In suka yi li'ani shi kenan ba aure tsakaninsu har abada.
TAMBAYA: Akaramakallahu. Dabba ce ta zo gidan mutum tun tana karama har ta yi girma ta haihu, sai ya kama uwar ya sayar. To ya hukuncinsa yake?
Daga Mustafa Ahmad Katsina.
SHAIKH ZAKZAKY: To, ita dai wannan dabbar dai ba tasa bace, ta mai ita ce. Saboda haka yana ajiye wa mai ita ne, duk ran da mai ita ya zo aka same shi, to zai mai da masa dabba, sai a biya shi ladan kiwo da sauransu. Saboda haka in ya sayar da wadansu saboda wani dalili kamar ya ga alamar za ta gaza, sai ya sayar, to har kudin ma na mai dabbar ne. Da fatan yana nan yana yi wa mai dabban ajiya, kuma yana nan yana cigiya. To har idan ya sami mai dabbar shi kenan sai sallama masa har da kudin wanda ya sayar din. In kuma bai samu ba, to daga karshe dai shi ba nasa bane, sai mu koma hukuncin kamar tsintuwa kenan, ya samu ya sarrafa wannan dukiya ta hanyar sadaka, da fatan Allah ya kai ladan ga mai wannan. Sai dai yana cire ladan kiwon da ya yi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mace na iya yin yayen danta, ko sai da yardar mijinta?
Daga Mustafa Ahmad Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Eh, idan ya cika lokacin yaye shi kenan. In ya cika shekara biyu shi kenan wa'adin yaye ya yi. Saboda haka ba sai ta nemi yardan mijinta ba. Amma in bai kai bane, to sai sun yi yarjejeniya tsakaninsu. Sai ya yarda, ta yarda ; dole ne su biyu su yarda kafin a yaye shi kafin shekara biyu.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne matarsa ta nemi da ya bar ta ta rika zuwa makaranta, amma ya hana, kuma shi ya ki ya koya mata. To yaya za ta yi?
Daga Mustafa Ahmad Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: To wajibi ne dai ta bidi ilimi. In ilimin nan na aikata wajibi ne, to shi ma bidarsa ya zama wajibi. Saboda haka in ya hana mata, to lalle ta samu ta tafi ko da bai yarda ba. Amma wannan zai fi kyau ya zamana ba kawai tafiyar za ta yi ba, sai ta kai shi kara, har ya zama a sasanta tsakaninsu, a nuna masa wajibin ya kyale ta ta bidi ilimi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. An ce idan mutum ya wayi gari da janaba azuminsa ya baci. Shin zai yi kaffara ne?
Daga Mustafa Ahmad Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: Idan da gangan ne ya bar janabar har lokacin da alfijir ya keto, to, lalle ramuwa da kaffara sun hau kansa. Amma idan da rashin sani ne masalan, to babu komai, sai ya yi wanka din. In kuma da mantuwa ne shi ma babu komai. Amma a dukkan wadannan ramuwa ne kawai ya hau kansa.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan mace ta sa kayan da Musulunci ya amince mata ta sa, kuma ta sa takalmi wanda idan tana tarfiya ana jin karar tafiyarta. Shin ta saba doka kenan ko kuwa?
Daga Ahmad Mairini Suleja jihar Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To, idan da ma shi wannan takalmin an yi shi ne don ya jawo hankali ya saba mana. A cikin Alkur'ani Allah (T) yana cewa, "kada su buga kafafuwansu don a san abin da suka boye na kayan ado." A wancan lokacin mata kan sa kwandagai a kafa, saboda haka mace bayan ta sa hijabi, in tana son a san tana da kwandagai na zinarori, sai ta buga kafanta, sai a ji su suna kara. Aka ce kar su yi haka nan. To, shi ma wannan buga takalmi mai kara ya so ya yi kama da shigen iren wadannan. In da ma shi takalmin yakan jawo hankali ne cewa ga mace na wucewa. Amma in wanda yake dama adatan ne, karar takalmi wanda bai sabawa al'ada ba. Kodayake shi wannan yana nufin na jan hankalin ne ko? Sai mu ce haramun ne kamar buga kafa don a ji adon kwandagai ne.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Wani ya shaida mani cewa, Malam ya ce idan mace ta zauna a wuri ta tashi, to kada ka zauna har sai wurin ya sha iska. To wannan ya yake?
Daga Sunusi Sulaiman Kasuwar Katsina
SHAIKH ZAKZAKY: To haka din ne yana daga cikin 'gara'ib' na hukunce-hukuncen mata, cewa yana da kyau idan mace ta tashi a wuri, kada namiji ba mijinta ba ya zauna, har sai ya yi sanyi.
TAMBAYA: Akramakallahu. Ko ya halasta na ba yaro nono alhalin ina cikin janaba?
Daga Atu Yusuf Gusau jihar Zamfara
SHAIKH ZAKZAKY: Ai ko da ya haramta, da shayarwa ta yi wahala. To lalle ba wani abu da aka samu dangane da haramcin ba da nono a yayin janaba. Bilhasali ma zamanin janaba yana iya daukar lokaci, shi kuma yaron yana iya yiwuwa ma da nonon ya dogara. A takaice dai shi nonon ba ya janaba.